ANA WATA GA WATA: Kotu ta garƙame Lauyan Sheikh Abduljabbar sakamakon zargin cin zarafi ga Kwamishinan harkokin addinan, Baba–Impossible.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Kotun Majistiri dake a Gidan Murtala ƙarkashin mai shari’a Hauwa Minjibir ta tura Lauya Hashim Hussein Hashim gidan gyaran hali sakamakon zargin da ake masa na zagin Kwamishinan harkokin addinai Tahar Adam (Baba Impossible).

Lauyan wanda shine mai baiwa Sheikh Abduljabbar kariya a shari’ar da ake gudanarwa tun watan Ogusta bisa zargin Shehin Malamin da cin zarafin Annabi (SAW) cikin wa’azin da ya gudanar a baya.

Kamar yadda Jaridar

Daily Trust ta wallafa, tun da farko dai Lauyan ya wallafa wasu faya-fayan audiyo wanda aka jiyo yana sukar Gwamnatin Kano bisa nuna rashin adalchi a shari’ar da ake gudanarwa kan Malam Abduljabbar, tare da bayyana cewa babu wurinda Malam Abduljabbar ya ci zarafin Annabi (SAW).

Sakamakon waɗannan kalamai na Lauya Hashim ne ya fusata Babban Limamin masallacin Juma’ar Kantin Kwari mai suna Albakari Mika’il ya maka Lauyan a kotu bisa zargin cin zarafinsa da kuma Kwamishinan addinai na Jihar ta Ƙano wato Baba-Impossible.

Har’ilayau, biyo bayan kama Lauyan da akayi a baya, shi ya sanya abokan aikinsa Lauyoyi sukayi tsayin daka tare karɓar belinsa da sharaɗin bazai ƙara wallafa audiyo ɗin ba; amma a ƙarshe aka ƙara jiyo shi ya wallafa tare da iƙirarin cewa Tahar Adam (Baba Impossible) bai cancanci a bashi Kwamishina ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *