Jarida ba za ta taba rayuwa a yankin mu na Arewa ba, littafi ba zai taba yin daraja a Arewa ba – Imam Sheikh Muhammad Nasir Adam.

Babban limamin Masallacin Juma’a na kofar Mata Imam Sheikh Muhammad Nasir Adam ya koka akan yadda al’ummar Arewa ba sa san yin karatu.

Limamin ya fadi hakan ne a hudubarsa ta Juma’a wadda ta gudana jiya a Masallacin Juma’a na Sheikh Ahmadu Tijjani dake unguwar kofar Mata a Kano.

Imam Muhammad Nasir Adam ya gabatar da huduba ne akan abubuwan da Annabi Muhammadu (s.a.w) yazo dasu.

Limamin ya ce babu shakka Annabi Muhammadu (s.a.w) ya zo da Ilimi, wanda kuma shine ginshikin cigaban kowacce al’umma.

Imam

Muhammad Nasir ya ce wahayin farko da aka yiwa Annabi Muhammadu (s.a.w) an umarceshi ne da yayi karatu.

Imam ya ce karatu shine hanyar samun ilimi, sai dai kuma ya koka akan yadda al’ummar Arewacin Najeriya ba sa son karatu, wannan dalili ne ma yasa Jarida ba za ta taba rayuwa a yankin mu na Arewa ba, littafi ba zai taba yin daraja ba a Arewa.

Ya kara da cewa kusan kowa a Arewa yana da Rediyo, Bahaushe yana da Rediyo, Babarbare da Bafulatani, Yaro da Babba, Mata da Maza kowa yana jin Rediyo a Arewa.

Imam ya ce kowane dan kasar Israel a kullum yana karanta a kalla shafi dari uku a cikin awa ashirin da hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *