Malaman addinai sun fi ƴan Siyasa illatarwa a Nigeria. ~A cewar Aisha Yesefu

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Fitacciyar ƴar Gwagwarmaya mai suna Aisha Yesefu ta ƙalubalanci Shuwagabannin addinai a Nigeria, inda ta ce sun fi ƴan siyasa muni.

Aisha Yesefu ta bayyana haka ne cikin wani saƙon mayar da martani da ta turawa Fasto William Kumuyi ɗaya daga cikin Malaman Majami’o’i a kudancin Nigeria.

Tun da fari dai Faston shine yayi rubutu a shafinsa na Twitter tare da nusar da jama’a akan su daina nuna ƙiyayya ga Shuwagabanni.

Daga nan ne kuma ƴar Gwagwarmayar ta fusata, yayinda ta mayarda martani a take tana mai cewa, “Shuwagabannin addinai sunfi ƴan siyasa ɓarna a Nigeria, sun mayarda mabiyansu kamar bayi suna amfani da addini domin biyan buƙatar kansu”.

A

ƙarshe, Yesefu ta yi kira cewa, idan mutane basu dawo daga rakiyar Fastoci, Malamai da Bokaye ba dole a cigaba da tafiya a wannan yanayin na ƙunci a Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *