Maulidi ba bidi’a bane sam, domin Annabi ne da kansa ya fara yin sa — Sheikh Halliru Maraya

Sheikh Halliru Maraya

Shahararren malamin addinin musuluncin nan ɗan darikar Tijjaniyya wato Sheikh Halliru Maraya, wanda yake zaune a Kaduna ya ce Annabi Muhammad SAW ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da aka fi sani da suna Maulidi.

Malamin ya shaidawa kafar sadarwa ta Bbchausa cewa:

“An tambayi Annabi Muhammad SAW dangane da azumin Litinin da ya ke yi. Sai annabin ya ce ranar ne aka haife ni”, in ji Sheikh Halliru.

Duk da sa’in sa da ake yi a farko, tsakiya da ƙarshen wannan wata mai albarka, akan halarci ko akasin hakan na Maulidi, malamin ya ƙara da cewa kamata ya yi Musulmi su kasance masu girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah S.W.A ya bai wa duniya kyautar da babu irinta watau samun haihuwar fiyayyen halitta Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

class="wp-block-image size-full">
Sheikh Halliru Maraya

Bugu da ƙari, babban malamin ya zayyano gamida lissafa wasu abubuwan da ya kamata a kasance masu gudanar wa a yayin Maulidi, inda yace:

  1. Taro domin nuna mu’ujizar Annabi da halayensa domin yin koyi da shi.
  2. Yin azumi
  3. Sada zumunci
  4. Ziyartar marasa lafiya a asibiti
  5. Yin sadaKa
  6. Ciyar da jama’a
Sheikh Halliru Maraya

Daga karshe malamin yaja hankali ga barin abubuwan da suka saɓawa shari’ar Muslunci ba, yayin gudanar da Maulidi, waɗannan abubuwa kamar yadda malamin ya bayyana sun haɗa da cakuɗuwar maza da mata, ihuce-ihuce, shaye-shaye da dai sauransu.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *