Mu rungumi halayen Annabi Muhammadu SAW, domin samun warhakar Matsalolin mu ~Cewar Sanata Uba sani.

A dai-dai Lokacin da ‘daukacin Al’umma musilmai ke cigaba da Murnar Zagayowar Ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW Sanata Uba sani wakilin kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya taya musilmai Murna da ganin wannan Rana Mai tsarki da albarka Sanatan Yana Cewa Ina yiwa ‘yan uwa amintattun Musulman Najeriya dama na duniya baki daya Barka da zuwa ranar Mauludin Annabi s.a.w tare da fatan Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da saukar da albarkar sa garemu Baki daya

A

Yayin da muke bikin tuna wa da wannan rana a Najeriya da duniya Baki daya bari mu yi amfani da wannan damar domin sake rungumar kyawawan halayen Annabi Muhammad (saw) domin samun warkar ga al’ummomin mu da sake gina tubalin tattalin arzikin cikin gida nageriya da yayi Matukar lalacewa.

Sanatan ya Kara da cewa Zaman lafiya da jituwa sun rabu da al’ummomin mu tun a lokacin da muka yanke kauna da haƙuri da juriya kuma muka maye gurbin su da ƙiyayya cikin Al’ummar mu ta zama cibiyoyin zubar da jini maimakon zaman lafiya”

Mun kyale ‘yan kasuwar bukata suna yin amfani damu domin yaki da juna mun fada tarkon na shirya manakisa gare mu Abin takaici Babu cigaba.

A dai-dai Wannan yanayi Bari mu yi amfani da wannan Rana ta maulidin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) domin sulhu da juna a tsakanin ƙabilu, addini da sauran lamuran da Ke sa rabuwar zamantakewa, tabbas mun Kasance mutane daya a gaban Allah. Mutunta juna da kauna za su sake dawowa Cikin Al’ummarmu daman can Ƙiyayya ce ta rage mu kuma ta lalata duk ci gaban da muka samu.

Ina rokon al’ummomi dake a duk fadin wannan kasar da su kafa masu sa kai na zaman lafiya wadanda za su samar wa matasa hanyoyin samar da fahimtar juna, magance rikice -rikice, inganta zaman lafiya da abota. Ingantaccen mu’amala da tattaunawa tabbas zai rage wannan inuwa ta rashin yarda da tabbatar da zaman lafiya da jituwa a tsakanin al’ummomin mu Inji Sanatan.

Sanatan da yake magana Kan kokarin da Gwamna Malam Nasir Ahmad El’rufa’i yake yi domin dawo da Zaman lafiya a jihar ta kaduna Ya kara da cewa Masoyin mu, Mallam Nasir El-Rufai ba wai kawai iya sake farfado da tattalin arzikin jihar Kaduna yake ba harda inganta hanyar raya muhimman ababen more rayuwa, tabbas yana kokari matuka wajen sake gina zaman lafiya a jihar tamu ta kaduna, Kwamitin Zaman Lafiya na Jihar Kaduna da Gwamna El-Rufa’i ya kafa kuma ya sadaukar da kai don inganta zaman lafiya ta hanyar tattaunawa baki ɗaya dole ne mutanenmu su goyi bayansa. Dole ne mu ba Hukuma duk goyon bayan da take buƙata don warware rikice -rikicen tare da ƙirƙira fahimta tsakanin mutanenmu. tabbas babu wani Abu a madadin zaman lafiya.

Ina jinjina ga masoyana mazauna yanki na mutanen kirki na shiyyar mazabar da nake wakiltar Kaduna ta tsakiya Kun kasance masu abin ban mamaki. Ina matukar godiya a gare ku. Ina bukatar ci gaba da goyon bayan ku tabbas Abubuwa masu kyau suna kan hanyar Zuwa gareku

Barka da Eid-el-Maulud

Sanata Uba Sani,
Kaduna Central Senatorial District

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *