Ni ba musulmi ba ne amma na san Annabi Muhammadu (SAW) shi ya fi kowa daraja a duniya- Chicharito

Ni ba Musulmi ba ne, Amma Na san Annabi Muhammadu Shi ne Mutumin da Yafi Kowa a Duniya Inji Chicharito

Duk waɗanda suka san shi saidai su faɗi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi.

Waɗanda suka karanta tarihinshi a natse, suna yawan yabawa tare da jinjinawa irin rayuwar da ya yi a duniya.

Chicharito ɗan wasan kwallon ƙafa ne na ƙasar Mexico wanda ya bayyana Annabi (SAW) a matsayin mutum mafi nagarta a duniya, duk da kuwa kirista ne.

Waɗanda suka sanshi ko suka karanta wani abu a kan shi, sun san irin albarkatacciyar rayuwar da yayi.

An gano cewa ƴan kwallo da sanannu a duniya na nuna mishi soyayya saboda tarihin shi da suka samu. Wanna ba kowa bane sai Annabi Muhammad SAW.

An turo shi ne zuwa ga mutane baki daya. Ba Annabin musulmai ba ne kaɗai, dukkan mutane ne za a musu hisabi da zuwanshi.

Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi.

A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da ya ke wa Manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.

Duk da ko Chicharito mabiyin Katolika ne, rayuwar Annabi ta matuƙar burgeshi har ya bayyana abinda ke ranshi.

Chicahrito ne ɗan kwallon kafa na farko a ƙasar Mexico da ya yi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya halarci wasan gasar kwallon kafa ta duniya a 2010. An karamashi bayan da yaci kwallaye 7.

Abun farin ciki ne da jin daɗi idan kaga wadannan mutanen suna karanta tarihin Annabi kuma sun bayyana kaunarsu gareshi. Allah ya kara tabbatar da mu cikin addinin musulunci da shiriya ta gaskiya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *