WATA SABUWA: Gwamna El-Rufai ya shatawa Malamai da Fastoci layi bisa salon yadda suke wa’azantar da mabiyansu.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kafa Kwamiti na musamman da zai rinƙa sanya idanu akan Malamai da Fastoci masu wa’azi a faɗin Jihar.

Binciken Jaridar Mikiya ya gano cewa tun a shekarar 2016 Gwamnan yayi yunƙurin aiwatar da wannan ƙudiri wanda yana cikin kundin tsarin mulkin Jihar kuma ya samo asali tun zamanin mulkin Soja wato Usman Muazu, sai dai a wancan loƙacin ƴan majalisun Jihar sun caccaki kuɗirin na El-Rufai wanda waɗansu suke ganin cewa yin hakan yunƙurin haramta gudanar da addini ne.

Hakazalika, a shekarar 2019 ƙungiyar Ƙiristoci mai suna (Pentecostal Fellowship of Nigeria) ta ƙalubalanci Gwamnatin ta El-Rufai a kotu, bayan share loƙaci ana shari’a a ƙarshe babbar mai shari’ah Hajaratu Gwadah ta yanke hukuncin cewa El-Rufai bashi da hurumin zanawa malaman addinai layi.

A

wannan karon ne kuma Gwamnan ya sake bijiro tare da yunƙurin sanya wannan doka, inda a ƙarshe ƙudirin ya samu amincewar majalisar dokokin Jihar ta Kaduna.

A ƙarshe, Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa dokar kula da ayyukan addinai wadda aka samar tun shekarar 1984 tana ɗauke da hukunce-hukunce masu tsauri ga duk Malami ko Malamin Mujami’ar da aka kama ya sauka layi yayin wa’azantar da mabiyansa.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *