Ya zama dole mu kawo karshen masu jujjuya mana fassarar Alkur’ani domin ra’ayin kansu ~Cewar Sarkin musilmai.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci hukumomin tsaro da shugabannin siyasa da su dauki matakin hukunta duk wanda ke tunanin za su iya juyar da kasar nan ta hanyar fassarar koyarwar addini.

Da yake magana a taron Ilimi na kasa na 2 na Sojojin Najeriya, wanda aka gudanar a Sakkwato, sarkin ya bayyana matsalar tsageranci.
Wanda ke sa ana jujjuya addini domin dacewa da ra’ayin su ba don a shiryar da su yadda ya kamata ba kan koyarwar, Gaskiya musamman na manyan addinan biyu. ”

“Wannan

babban kalubale ne a gare mu. Don haka ilimi yanki ne guda ɗaya da za mu iya magance ƙalubalen tsattsauran ra’ayi.

Ya kamata kuma kada mu ƙyale masu tsattsauran ra’ayi su mamaye kowane yanki na ƙasar nan kuma dole ne mu yi hakan ta hanyar ƙalubalantar su ta fuskar ilimi da tsaro, ”in ji shi.

Sarkin ya ce taron yana zuwa ne a lokacin da ya dace musamman duba da yawan kalubalen dake fuskar tar kasar.

Sarkin Musulmin ya ce rashin aiwatar da kudurorin da aka cimma a irin wannan taro shi ne dalilin da ya sa Najeriya ta fada cikin matsaloli daban -daban.

“Da’ace Muna haduwa don tattauna matsalolin mu, da yawa mafita za ta zo kuma mafi alkhari ga kasarmu

Ya kuma shawarci cewa, ya kamata a koyar da darussa cikin harsunan yarukanmu na gida nageriya yana mai cewa hakan zai sa daliban mu su yi karatu da kyau da sauri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *