Ziyarar Ta’aziyya da Jaje: Pantami ya wakilci Buhari zuwa ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Ya tabbatar masa da Gwamnati ta bada umurni a binciki masu laifi.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Ya wakilta Malam Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci izuwa ga ta’aziyya ga Shaykh Dahiru Usman Bauchi, bisa kisan gilla da akayi wa dalibansa.

Sannan kuma a tabbatar masa da Gwamnati ta bada umurni a binciki masu laifi, a musu hukunci kamar yadda doka ta tsara.

Malam Pantami ya gana da Shaykh Dahiru Bauchi, sannan ya isar da ta’aziyya ga Shaykh.

Bugu

da ƙari, kuma Shugaban Ƙasa zai gana da Shaykh Dahiru in Allah Ya yarda bayan kammala zaman Kaɗaitaka da yake da dokar Covid-19 ta tanadar biyo bayan tafiyar da yayi.

Muna adduar Allah Ya jikan bayinsa da suka riga mu gidan gaskiya. Ya gafarta masu, sannan Ya sa Aljannah ce makomarsu da mu baki daya.

Kuma Allah Ya kawo karshen tashin hankali a Nijeriya, Ya kuma tona asirin masu tayarwa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *