Zuciyar dake son Annabi SAW ba zata Shiga wuta ba ~Cewar Sheikh Nuru Khalid.

Shahararren malamin Addinin Islama limamin masallacin Apo legislative Courters dake Abuja ya halarci maulidin Annabi Muhammadu SAW a Garin mararaban Abuja da jihar Nasarawa duk da Cewa malamin ‘dan Aqee’dar Salafiyya ne amma ya halarci maulidin ya kuma hau mimbarin wa’azi tare da fadakar da juna Cewa Kan mahimmanci soyayyar fiyayyan halitta SAW inda malamin Yace duk zuciyar dake son Annabi Muhammadu SAW ba zata Shiga wuta ba ya Kuma yi wa’azi tare da bayyana mahimmancin ha’din Kan Al’umma musilmai musamman a wannan yanayi da Musilmai ke Cikin kalubale.

Ga

dai kadan daga bidiyon maulidin na shehin malamin…
https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/11/YouCut_20211101_090548865.mp4

Ba a Saba ganin wani malami daga bangaren Salafiyya Izalah sun halarci bikin maulidin Annabi Muhammadu SAW duba da Cewa ya sabawa Aqee’dar su Amma zuwan malamin wajen taron maulidin ya sa Jama’a da dama tofa albarkacin Bakin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *