Bayan zama na Biyu, Kotu Ta dakatar da Rantsuwa a wajan bikin nadin sabon Sarkin Zazzau.

Mai martaba, Alhaji bashir Aminu dan iyan zazzau ya kai karar gwamnatin jihar kaduna kan nadin sabon sarkin zazzau bayan rasuwar marigayi shehu Idris.

A cewar Bashir zabin gwamnan baya cikin jerin sarakunan masarautar zazzau.

Bayan wannan, kotu a kaduna ta dakatar da sabon sarki daga amsa sunan sarkin zazzau a ranar 16 ga Oktoba bayan fara sauraron karar.

Wannan bai canza komai ba, kwanan nan ya ziyarci mai alfarma sarkin sokoto, Saadu Abubakar sannan kuma ya bayyana a matsayin sarkin Zazzau.

Bayan sauraro na biyu a kaduna kotun kuma ta dakatar da rantsar da sabon sarki da aka nada, Ambasada Nuhu Bamalli Kotun ta kuma ce za ta iya yanke hukunci na karshe ne kawai bayan ta ji daga bangaren wanda ya shigar da karar wanda shi ne iyan zazzau Alhaji bashir Aminu.

Al’umma

da dama suna ganin abin takaici ne yadda gwamnoni suka tsunduma cikin nuna son kai lokacin da ya shafi nada sarakunan gargajiya.

Nadin da ake yi yanzu a najeriya ba ya dogara da cancanta ko nasaba, ya danganta da wanda ka sani kuma waye ya san ka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *