Mai wasa da kura da biri ya sheƙe kan yaro da wata zabgegiyar kokara

Wasu masu wasa da kura sun yiwa wani yaro illa tare da yi masa rauni, yayin da suke gudanar da sana’ar su ta wasa da kura da biri a can yankin sabuwar Gandu dake ƙaramar hukumar Kumbotson jihar Kanon Najeriya.

Muhammad Sani, shine ɗan uwan yaron da aka yiwa rafkiya da kokarar, ya faɗawa wakilin mu cewa, suna cikin wasa da kura ne, sai suka soma koran yara daga wajen, wanda a saboda haka ne yaron ya amshi rabon sa.

To sai dai fa kokarar tayi illa ga yaron, domin tuni jini ya taru a idonsa, kuma an garzaya dashi asibiti domin ya samu agajin gaggawa.

Mai wasa da kura tuni ya shiga hannu, amma an nemi mai wasa da birin sama ko ƙasa an rasa, domin tuni ya cika wandon sa da iska.

Da mai kura yake zantawa da manema labarai, yace, shi atafau ba bashine ya daki yaro ba. Ga kalaman sa:

“Wallahi mai gida sana’a muke akace yaro yaji rauni, Ni kuma ban ɗaga wani abu na doke shi ba.”

Yanzu haka dai yana hannun jami’an tsaro inda ake cigaba da faɗaɗa bincike.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *