Muhammad Sanusi II ya cika shekaru (60) cif a Duniya.

Sarki Muhammadu Sunusi Na ll

Me kuka sani game da rayuwarshi?

Shine ya fara kawo tsarin bankin musulunci a Najeriya, sannan ya taɓa zama shugaban babban baki mafi ƙwazo a duniya. I

Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi II, an haife shi ranar 31 ga watan July na 1961.

Ya yi karatun ilimin addini mai zurfi da na Boko.

Ya kasance haɗaɗɗen masani a ɓangaren ilimin tattalin arziki, kuma shahararren malamin addinin musulunci ne, wanda har yakai ga zama halifan Tijjaniyya.

Bugu

da ƙari, ya taɓa zama shugaban babban bankin Najeriya (CBN daga 3 ga watan june zuwa February 2014).

Shine ya fara kawo tsarin bankin musulunci a Najeriya, sannan ya taɓa zama shugaban babban baki mafi ƙwazo a duniya, duk a lokacin da yake riƙe da wannan muƙamin.

Ya zama Sarki a Kanon dabo, a ranar (8 june 2014). Ya sauka 9 ga watan March, 2020.

Jagora ne mai shugabantar ƙungiyoyi kala kala, domin kawo cigaba ciki da wajen ƙasar nan.

Bincike dai ya nuna cewa, Sarki Muhammadu Sanusi II shine Sarki, wanda aka fi so, ƙauna da shauƙi daga ɓangaren talakawa, masu kuɗi, fadawan Sarki da sauransu. Domin arewa, Indai sarauta ce, ado, iya magana, taku da ilimi, samun irin sa sai an yi gumin goshi.

SHEKARU MASU ALBARKA MUHAMMADU SANUSI II.

Shin da wani abun alkairi zaku iya tunashi?

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *