Nigeria na daga cikin jerin ƙasashen da akewa mata auren wuri a Duniya; kaso 78% cikin 100% ana yi musu aure ne kafin shekaru 18. ~Bincike

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Kungiyar kula da harkokin yara SCI mai reshe a Amurka ta bayyana cewa kaso 78% cikin ɗari 100% na yara-mata a Nigeria ana yi musu aure kafin cika shekaru 18.

Ƙungiyar ta tattara wannan bayanai ne bayan bincike na tsanaki tare da wallafa cewa anfi samun wannan al’amari a Jihohin Arewa maso yammaci da kuma gabashin Nigeria.

Sa’innan kaso 45 cikin 78 anayi musu aure kafin shekaru 15.

Rahoton ya kuma ƙara da cewa wannan dalilin ne ya sanya Nigeria ta kasance a cikin jerin ƙasashe masu yiwa yara mata auren wuri a faɗin Duniya. Wanda hakan ne yake hana su samun damar yin wadataccen karatu zamani da na Addini.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *