Ba zan sake ‘daukar Hoto da kai ba idan ba zaka saki fuska kayi murmushi ba ~Mansura ta faɗawa tsohon mijinta sani danja

Tsohuwar matar sani Musa danja mansura Isa ta gargadi sani Musa danja Cikin barkwanci Cewa ba zata sake daukar hoto tare dashi ba Matukar ba zaiyi murmushi ba Hakan ya biyo bayan wani hoto da Suka dauka Daren Ranar Asabar a Platinum Cinema Dake Kano a Lokacin da Suka je kallon film din FANAN a Hoton Ranar asabar an hango sani Musa danja tare da tsohuwar Jarumar Kuma tsohuwar Matarsa sun dauki hoto a tare Amma fuskar sani Musa a turbune Babu murmushi Lamarin da yaja hankulan masu bibiyar mansura suna cewa meyasa sani danja Bai saki muryarsa yayi murmushi ba?

class="wp-block-image size-full">

A Daren jiya ne mansura tare da sani danja Suka sake haduwa a platinum cinema wajen kallon film din na FANAN.

Mansura Isa ta wallafa hotuna Cikin nishadi tana cewa kuji Abin mamaki, Muna Nan munayi sani danja gargadi kafin na saki hoto, nayi hoto dashi na saki a jiya amam Mutane suna korafin bashi yin murmushi,

Ni da ‘dan uwana hafizu Bello, na fada Masa idan ba zai Yi murmushi ba bazan sake daukar Hoton dashi ba, bazan Zo na kashe kaina ba ko dai yayi murmushi ko Kuma na tsere na bashi waje.

Jama’a da dama na cigaba da tofa albarkacin Bakin su Kan Wagga Al’amari.

Sani Musa danja da mansura Isa sun Kasance ma’aura ta sama da tsawon Shekaru goma kafin labarin rabuwar aurensu ya zageye yanar gizo-gizo a wattani Hudu da Suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *