Azima ta bayyana bukatarta ta neman mijin Aure, ta ce kuma da gaske take.

Spread the love

Wata matashiya mai suna Azima Yusuf ta bayyana bukatarta ta neman mijin Aure nagari.

Azima ta wallafa bukatar tata ne a shafinta na Twitter, inda ta nemi jama’a da su tayata da Addu’a Allah yabata miji nagari.

Azima ta rantse cewa dagaske take, Aure takeso.

A kalaman nata, Azima tace “Da Allah ku sani cikin addu’a, Allah ya bani miji nagari😭🙏🏼 wlh da gaske Aure nake buƙata” kamar yadda ta rubuta a shafin nata na Twitter.

Azima dai kyakkyawar mace ce, son kowa kin wanda yarasa kamar yadda kuke gani a hotunanta da muka wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *