A daidai lokacin da ɗaliban jihar Kano ke kokawa akan rashin samun sakamakon jarrawar NECO, Gwamnatin Kano ta ce ta samar da isassun kudi domin aiwatar da tsarin Ilimi kyauta kuma dole a shekarar 2022.

Gwamnatin jihar Kano ta samar da isassun tanadi a kasafin kudin 2022 domin samun nasarar aiwatar da manufofin ilimi kyauta da tilas a jihar.

Kwamishinan Ilimi, Sunusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kare kasafin kudin ma’aikatar ta 2022 a zauren majalisar dokokin jihar Kano.

Ya yi nuni da cewa, manufar za ta bukaci a samar da dimbin albarkatu domin daukar nauyin miliyoyin yara, musamman wadanda ke karkashin kasa domin cimma manufofin da ake so.

“Gwamnatin

jihar ta ware kaso mai tsoka na kasafin kudin 2022 ga bangaren ilimi ciki har da ma’aikatar ilimi mai zurfi domin yaki da jahilci da rashin aikin yi a tsakanin al’umma,” inji shi.

Sai dai Kiru ya bayyana cewa majalisar ta yi alkawarin taimakawa ma’aikatar ta kasafin kudin shekarar 2022 domin baiwa bangaren damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *