A karon farko Jami’ar tarayya dake Dutse (FUD) ta baiwa ɗalibai 4,290 guraben karatu a wannan shekarar ta 2020/2021.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Shugaban makarantar mai suna Farfesa Abdulkarim Muhammad shine ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ake gudanar da bikin rantsar da sabbin ɗaliban da Jami’ar ta baiwa guraben karatu a fannoni daban-daban.

A yayin jawabin nasa, yayi kira ga ɗaukacin ɗalibai musamman waɗanda suka samu nasarar samun guraben karatu akan su mayar da hankali wajen bin doka da oda, karanta littafai tare da zama ɗalibai nagari.

Farfesan ya ƙara da cewa, “Jami’ar ta Dutse (FUD) tana ɗaya daga cikin Jami’o’i da yanzu ake rububi a Nigeria, domin akwai ɗalibai sama da dubu 20,153 da suka nemi gurbin karatu amma kaso 20% kawai suka yi nasarar samun guraben karatu a makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *