A safiyar yau wasu makarantu a Abuja sun bukaci iyaye da su ajiye ‘ya’yansu a gida har sai an sami tsaro.

Sanata Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya ce a safiyar yau wasu makarantu a Abuja sun bukaci iyaye da su ajiye ‘ya’yansu a gida har sai an sami tsaro, Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar yau.

Wata kila hakan yana da nasaba da sace malamai da ɗalibai a Jami’ar Abuja.

Lamarin

tsaro ya tabarbare a yabkin Arewa ta tsakiya, inda masu garkuwa da mutane suke yin garkuwa da ‘yan makaranta da sauran jama’ar gari don neman kudin fansa.

Sanata Shehu Sani ya yi kaurin suna wajen caccakar gwamnati akan rashin tsaro, shiyasa ma mutane da dama suke ganin ya wallafa sakon ne don ya nuna gazawar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a fannin samar da tsaro ga ‘yan Ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *