An kasa tura ‘yan bautar kasa zuwa kananan hukumomi 11 a Jihar Neja saboda Tsoron ‘yan ta’adda.

Sakamakon karuwar hare-haren ‘yan fashi da makami, Hukumar NYSC ta Jihar Neja ta ce ba za ta iya tura yan bautar kasa zuwa kananan hukumomi 11 daga cikin 25 don aikin su na farko a jihar.

Darakta, a Hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) reshen jihar Neja, Hamza Audu ne ya bayyana hakan a Minna yayin ziyarar tawagar sa ido daga Ma’aikatar Harkokin Agaji da Kula da Bala’i ta Tarayya zuwa jihar don lissafa ɗalibai da masu dafa abinci a ƙarƙashin Shirin Ciyar da Makaranta har Gida ta gwamnatin tarayya.

Daraktan

NOA na jihar ya yi bayanin cewa don kar a jefa rayuwar membobin bautar kasa, NYSC ne jihar ta yanke shawarar ba za a tura su kananan hukumomi 11 da ke fuskantar hare -haren ‘yan bindiga ba.

Ya yi bayanin, “muna amfani da mazauna yankin a makarantun da abin ya shafa, waɗanda ke yi tattaunawa da mazauna yankin don kada su jefa rayuwar membobin NYSC cikin haɗari.”

Hakanan, Hajiya Fatima Bisalla, wacce ta jagoranci tawagar sa ido daga Ma’aikatar Agaji da Kula da Bala’i ta Tarayya ta shaida wa manema labarai cewa sun kawo ziyarar ne domin baiwa Ma’aikatar damar samar da bayanai kan wadanda suka ci gajiyar Shirin a Jihar.

“Gwamnatin tarayya tana son sanin adadin ɗalibai da masu dafa abinci a kowace jiha kafin mu haɓaka shirin don haɗa ƙarin ɗalibai a watan Satumba.

Ta ce, kungiyar ta gamsu da abin da ta gani a kasa a Neja dangane da bayanan da jihar ta gabatar kan shirin ciyar da makarantu, ”in ji ta.

Bisalla ta ci gaba da bayyana cewa ana gudanar da aikin kidayar ne dangane da hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) da kuma hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Da yake jawabi, mai kula da shirin na jihar, Bar. Amina Gu’ar ta lura tare da gamsuwa da ingancin abincin da ake ba wa ɗalibai a jihar.

“A halin yanzu, muna da ɗalibai 560,000 daga makarantu 3,032 da ke cin gajiyar shirin a jihar. Kuma, muna da masu dafa abinci sama da 5,000 da ke yiwa ɗalibai a fadin jihar ”, in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *