Bayan an kai ruwa rana, a karshe Ganduje ya biya kudin jararabawar NECO na daliban sakandire.

A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2021 da hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta yi, bayan ta rage basussuka.

Daliban makarantun gwamnati da suka fito daga jihar Kano sun kasa samun sakamakon nasu a lokacin da aka sake su makonni uku da suka gabata saboda basussukan da hukumar NECO take bin jihar na sama da Naira biliyan 1.8.

Sai

dai a wata sanarwa da ta fitar a Kano yau Lahadi, ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce a yanzu dalibai za su iya duba sakamakonsu domin yanzu haka an sake su.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Aliyu Yusu, ta ce: “Wannan ya biyo bayan kokarin da ma’aikatar ilimi ta jihar ta yi na samun kudade daga gwamnatin jihar domin biyan kudaden jarabawar NECO.”

Fitar da sakamakon a cewar kwamishinan ilimi na jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, zai baiwa daliban damar samun damar shiga jami’o’i da sauran manyan makarantun da suka ga dama.

A yayin da ya bukaci daliban da su yi amfani da katinan rajista wajen shiga da kuma buga sakamakon jarrabawar, ya kuma yi kira ga jama’a da su sanya dabi’ar nuna godiya ga abin da gwamnati ke yi duba da irin kalubalen da ake fuskanta kan karancin albarkatun da take da su.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na ci gaba da tallafawa fannin ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *