•Cin Zarafin Mutane a yanar gizo (Cyber-stalking / Cyber-bullying)

• Daurin Sheakara 10 Ko tarar Miliyan 25 Shine Hukuncin Cin Zarafin Mutum a Social Media koda Mutumin kuwa ba yada rai.


Me ake nufi da Cyber-Stalking /Cyber-bullying ?

Cyber-Stalkig ko Cyber-bullying ana amfani dasu a matsayin abu daya wato shine: “Cin Zarafi ko mutuncin wani a yanar gizo (Internet) da suka hadar da: Facebook, Twitter, Instagram, Telegram, WhatsApp Text Message da sauran su”

Wasu

kuma sukan dauki cewa Cyber-Stalk shine uwa, wato “General term” na laifuffukan Cin zarafin mutane a yanar gizo, wanda a karkashin sa akwai irin su: “Slander” “Defamation” “False Accusations” “Trolling” da sauran su.

Cin zarafi ko mutuncin mutane a yanar gizo abune da ya zama ruwan dare gama duniya, ta inda kaso mai yawa daga cikin marubutan mu suke cin zarafin mutane a yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani watakila dan su samu “Comments” ko “Like” ko kuma su samu Shahara (Popularity) ba tare da tunanen cewa Suna gayyatowa Kansu rigima bane ba tare da sun sani ba.

Cin Zarafin Mutane laifi ne da dokar Musulunci tayi hani a kansa, kuma munga hakan a cikin ayoyi da hadisai masu yawa a karkashin Dokokin Shari’ar Musulunci (Islamic Law) hakan ne yasa kasar mu ta gado (Nigeria) ta dauki matakin ba-Sani-ba-sabo ga duk mutumin da ta samu da Wannan laifin na cin zarafin mutane a yanar gizo.

Wasu daga cikin Hanyoyin da Za’a iya cin zarafin mutum a Yanar gizo:
1• Tura maka Sakon tsoratarwa ko barazana ta hanyar Sakon Kar ta kwana (Text Message)

2• Bibiyar Mutum dan ka gano Wasu boyayyun laifukan sa ko wasu bayanan sa da suka shafeshi saika rika turawa mutane ko kuma kayi Posting dinsu dan ka kunyatar dashi.

3• Ka dauki wayar mutum ko Computer ka tura wasu sakuna na karya da zummar cewa mai wayar ko Computer din ne yayi.

Kamar yadda yazo a Sashi na 24 (a) da (b) a cikin baka na Kundin Hana fasa Kwabrin yanar gizo, 2015 (Cyber Crime Prohibition Act, 2015) cewa: “Duk wanda ya yada wata magana ta karya don ya bata wani, ko ya zagi wani, ko yasa aka zageshi, ko yasa aka tsaneshi, ko aka tsangwameshi, ko aka cutar dashi, ko ya yada hoton tsiraicin sa, da sauran su” to ya aikata cin zarafi a Yanar gizo.

Har wayau dai Sashi na 24, Karamin Sashi na 2, (a) (b) da (c) a cikin baka na Wannan kundin yace: “Duk wanda ya yada wani Sako (Kuma yana sane, kuma da niyyar hakan, sakon hoto ne, Video ne ko rubutu ne) ta hanyar Computer, ko yanar gizo ko wayar Salula, dan yaci mutuncin wani, ko ya saka shi cikin razani/firgici/ tsoro, Har ya zama wannan mutumin yana tsoron zai iya rasa ransa, ko wasu zasu iya cutar dashi sakamakon Wannan rubutun da akayi akan shi, ko hoton nashi da aka yada a yanar gizo, ko kuma yana tsoron za’a iya Sace shi, to ka aikata laifin cin zarafi a yanar gizo, Hakanan koda Matacce ne kaci mutuncin sa to za’a daukeka a matsayin wanda ya aikata laifin Cin Zarafi ta yanar gizo” Shari’ah zata bimasa hakkin sa tare da ko baya Raye a duniya.

Wannan kundi na “Cyber Crime Prohibition Act, 2015” yazo da hukunci mai tsanani akan wannan laifi, domin tabbatar wa sai mu duba:
Sashi na 24, karamin Sashi na 2, (a) a cikin baka, Sakin layi na daya (i) zamu jishi yana cewa:
“Duk wanda ya aikata wannan laifin ”na cin zarafin mutane a yanar gizo” za’a daureshi a gidan Maza (Prison) Har na tsawon Shekara 10, Ko kuma a tilasta masa biyan tarar kudi da suka kai Naira Miliyan Ashirin da Biyar 25,000,000,00 (25 Million).

Wanna Shine hukuncin.

Abubuwan da ya kamata kayi a duk Lokacin da akaci Zarafin ka a Yanar gizo.
1• Daga Lokacin da akaci Zarafin ka a Yanar gizo to kayi kokarin kai koken ka wajen Kamfanin Sadarwar (Sannan Kuma kayi Screenshot din koken daka kai).

2• Kayi Sauri Kayi Screenshot din rubutun cin zarafin ko hoton ko videon ko sakon, dan kar ya goge ko kuma ya canja.

3• Ka nemi Shawarar Lauya domin sanin yadda zaka bibiyi hakin ka.

4• A karshe sai kaje Kotu dan Shigar da kara.

Allah ya kyauta, Amin !

Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
19th November, 2021.

One thought on “•Cin Zarafin Mutane a yanar gizo (Cyber-stalking / Cyber-bullying)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *