Gwamna Ganduje ya baiwa wani Makaho mai suna Ɗahuru gurbin aiki, inda zai rinƙa koyarwa a makarantar Firamare bayan shafe shekaru yana koyarda ɗalibai ba tare da ko sisi ba.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Gwamnatin Jihar Kano, ta baiwa makaho Dahuru Abdulhamid Idris, gurbin koyarwa.

Wannan rahoto yana ƙunshe cikin wani bayani da Kwamishinan Ilimin Jihar, Alhaji Sanusi Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust tayi fira da wannan Makaho, Dahuru ya kasance makaho, amma a hakan bai dakayarda da shi wurin yin karatu ba, domin a shekarar 2017 ya kammata NCE.

Tun bayan da ya kammala NCE, Dahuru ya bayyana cewa bai samu damar yin aikin komai ba. Amma a hakan ya cigaba da zuwa makarantar Firamaren Unguwarsu inda yake karantar da ɗalibai yaren Turanci.

Tun

da fari dai Jaridar Daily Trust ne sukayi fira da wannan makaho, wanda daga nan ne bidiyon ya shiga garari a shafukan sada zumunta; ayau ne kuma Gwambatin ta Jihar Kano ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatarda baiwa Dahuru gurbin aiki, inda zai rinƙa koyarwa a makarantar Firamaren Tudun Maliki dake ƙaramar hukumar Tarauni a Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *