Hukumar NECO ta saki sakamakon jarabawar wannan shekarar ga ɗalibai.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Hukumar jarabawar NECO ta saki sakamakon jarabawar musamman ga ɗaliban da suka rubuta a wannan shekarar.

Babban Rijistara a sashin, mai suna Farfesa Dantali Wushishi ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Juma’a a babbar helkwatar NECO dake garin Minna, Jihar Neja.

Ya bayyana cewa, a cikin kaso 100% na ɗaliban da suka yi rijista, kaso 97% sun samu damar rubuta jarabawar.

Mista Wushishi ya ƙara da cewa ɗalibai da dama sun samu sakamako mai kyawu idan aka kwatanta da shekarun baya.

A ƙarshe kuma ya bayyana gamsuwarsa game da yadda tsarin jarabawar ya gudana a cibiyoyi daban-daban dake faɗin Nigeria.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *