Kwalejin tarayya dake Jihar Bauchi (Poly) ta tabbatarda korar Malamai biyu sakamakon gano su da laifin cin zarafin ɗalibai da hanyar lalata.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Hukumar gudanarwar Kwalejin Jihar Bauchi ta tabbatarda korar malamai biyu sakamakon zarginsu da ake na cin zarafin wasu ɗalibai ta hanyar lalata.

Malam Sunusi Gumau shine ya bayyana hakan ga manema labarai yayin zama na 98 da hukumar makarantar ta gudanar ayau Lahadi.

Mista Gumau ya bayyana cewa, wannan mataki ya tabbata ne biyo bayan bincike na tsanaki da aka gudanar dangane da al’amarin.

Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta wallafa, malamai biyun da aka kora sun haɗa da Abubakar Baba Malami a fannin ilimin abinci (Nutrition) sai kuma Adebusoye Sunday mai aiki a fannin ilimi a taƙaice.

Har’ilayu,

Mista Gumau ya ƙara da cewa, tun da fari sun kafa kwamiti domin gudanar da bincike na tsanaki tare da tabbatarda sahihancin al’amarin. Amma bayan wannan, su waɗanda ake zargi da wannan mummunar ɗabi’a babu wanda ya iya kare kansa da gamshasshiyar hujja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *