Minista Pantami bai cancanta ya zama Farfesa ba. ~A cewar ASUU

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Ƙungiyar Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta ƙalubalanci naɗin zama Farfesa da akayima Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Pantami.

Kamar yadda Jaridar The Nation ta rawaito, tun a baya dai Shugaban makarantar mai suna Farfesa Mohammed Abdulaziz shine ya aika saƙon taya murna ga Pantami bisa naɗin, yayinda daga baya kuma Ƙungiyar Jami’o’in ta nuna rashin gamsuwarta dangane da sahihancin al’amarin.

Makarantar ATBU ta kasance tsohuwar makarantar da Minista Pantami ya halarta kuma a baya ma ya taɓa koyarwa a matsayin lakcara.

Wannan rahoto yana ƙunshe cikin wani bayani da wakilin ASUU reshen Jihar Bauchi mai suna

Dr Ibrahim Inuwa ya wallafa. Inda ya ƙara da cewa “wajibi mutum yabi wasu matakai a sahihance kafin a tabbatar dashi a matsayin Farfesa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *