Musan Doka: Duk Wanda Yaji Taken Najeriya Bai Tashi Tsaye Don Girmamawa Ga Kasa Ba, To Ba Shi Da Mutunci A Idon Doka.

Shashi na 34 na kundin tsarin sashi ne da yake magana akan ‘yancin kare mutuncin Da’adam da kuma abin da yake sawa mutuncin mutum yazube a idon doka.

Dokar tana bayani akan yadda kowane Dan Kasa yake da mutunci da kima da kuma ‘yancin kare mutuncinsa, ta hanyar hana kowa taba dukkan abin da ya shafi mituncinsa.

To sai dai kuma daga an zayyano wasu abubuwa suke janyowa mutuncin mutum yazube a idon doka.

Ga

su kamar haka:-
1- Wanda aka yankewa halastaccen hukunci a kotu ta hanyar horar da shi da wani aiki. Misali: Fasa dutse ko bulala, to wannan ba shi da rigar mutunci a doka.

2- Sai kuma wanda ake tuhuma da wani laifi a kotu kafin a yanke masa hukunci, shima wannan ba shi da rigar mutunci a doka, tunda kamashin nan da akayi ai ka ga an taba mutuncinsa.

3- Sai kuma wanda ya karya ko yayi kokarin karya dokar kasa, daga lokacin da ya karya wannan dokar to ba shi da mutunci a idon doka. Saboda bai mutunta dokar kasa ba.

4- Ko kuma wanda yaji anyi taken Najeriya (National anthem) yaki tashi tsaye shima wannan ba shi da mutunci a idon doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *