Tsohon shugaban kasa Goodluck ya samu sabon mukami.

Tsohon shugaban kasa Goodluck ya samu sabon mukami.

Kwanan nan aka nada tsohon Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan a matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish University Uganda (CUU).

Nadin na daga cikin sanannun martabar duniya da aka baiwa tsohon shugaban.

Jami’ar Cavendish Uganda wacce jami’a ce mai zaman kanta tana ɗaya daga cikin manyan Jami’o’in Afirka.

Jami’ar ta fara aiki a shekarar 2008. A wajen bikin budewar, tsohon Shugaban kasar Zambiya, marigayi Kenneth Kaunda shi ne Shugaban Jami’ar.

CUU

tana da alaƙa da Cavendish College London, Cavendish University, Tanzania da Cavendish University, Zambia. An fara bikin kammala karatun a makarantar a watan Nuwamba 2011.

Jami’ar na da cibiyoyi daban-daban a duk fadin kasar ciki har da harabar jami’a a babban birnin kasar na Kampala.

Jami’ar ta rubuta a Facebook;

“Maraba da zuwa Goodluck Jonathan yayin da ka karbi ragamar Shugabancin CUU. Muna fatan wannan samun cigaban zamanin da cimma manyan abubuwa a karkashin jagorancin ka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *