Za’a buɗe Jami’ar Jos makwanni 7 bayan rufe makarantar sakamakon rikicin da ya ɓarke a Jihar Filato cikin watan Ogusta.

Rahotanni sun tabbatarda ranar 11 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za’a cigaba da gudanarda jarabawar zangon karatu na farko a Jami’ar Jos (University of Jos).

Hukumar gudanarwar makarantar ce ta bayyana haka yau Alhamis bayan shafe makonni da rufe makarantar sakamakon rikicin da ya faru a birnin Jos na Jihar Filato a watan Ogusta, wanda yayi sanadiyar mutuwar aƙalla biyu daga cikin ɗaliban makarantar.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *