ƴan ta’addan da suka yi ƙoƙarin hambarar da gwamnatina suna Najeriya — inji shugaban ƙasar Turkiyya, Erdogan.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya nuna damuwa cewa har yanzu ƙungiyar ƴan ta’adda ta Fetullah (FETO), wanda ake zargi da laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016, ya ci gaba da aiki a Najeriya.

Erdogan ya yi magana ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa tare da Shugaba Muhammadu Buhari a yayin ziyarar aiki a Najeriya.

A cikin jawabin da ya gabatar a cikin yarensa na Turkiya kuma ɗaya daga cikin jami’an da ke tawagarsa ya fassara shi, Erdogan ya nemi Najeriya da ta shiga ƙasarsa don samar da haɗin kai a yaƙi da ta’addanci a kasashen biyu a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin ƙawayen Turkiyya a Afirka duba da ganin ƙasashen sun ɗauki kimanin shekaru 60 na dangantakar diflomasiyya.

class="wp-block-image size-full">

Ya ce: “Manyan ƴan jarida, a matsayinmu na Turkiyya, muna nan muna sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, ƴan uwanmu da kuma abokan mu.

“Kungiyoyin ƴan ta’adda, gungun masu ɗauke da makamai da kuma ƴan fashin teku na ci gaba da aiki a Najeriya kuma hukumomin Najeriya na ci gaba da yaƙar su. Don haka, don ba da haɗin kai a fannonin soja da tsaro, muna yin duk abin da yake mai yiwuwa….

“Kamar yadda wataƙila muna sane da cewa Turkiyya tana yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci shekaru da yawa, kamar PKK, PYD, FETO, DASH da sauran ƙungiyoyin ta’addanci.

“Waɗanda suka aikata mummunan juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga Yuli, FETO, har yanzu suna nan suna aiki ba bisa ka’ida ba a Najeriya, kuma muna ci gaba da musayar bayanan sirrin mu ga masu tattaunawa da hukumomi na Najeriya. Ina fata da addu’a cewa ƴan uwanmu na Najeriya za su ƙulla haɗin kai a wannan fanni tare da mu, Jamhuriyar Turkiyya. Ina fata da addu’a cewa ziyarar tamu za ta ba da sakamako mai kyau kuma ina son in gode wa fitaccen ɗan uwana, Shugaba Buhari, saboda kasancewarsa mai masaukin baƙi mai matukar haɗuwa a gare ni da wakilai na ”, in ji shi.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *