A wani salon tursasawa, wani mutumi ya kashe matarsa saboda ta ƙi musulunta.

Ana zargin wani mutum da kashe matarsa mai shekara 28 a ƙauyen Churai Dalpatpur a a Indiya saboda ta ƙi yarda da tursasawarsa na dole ta musulunta.

Ƴan sanda a Mirgani sun ce suna tsare da mutumin.

An samu gawar matar mai suna Nisha a rataye a ɗakinta a ranar Talata cikin dare, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.

Babban jami’in ƴan sandan yankin Raj Kumar Agarwal ya ce binciken da aka gudanar ya nuna ta mutu ne ta hanyar shaƙure wuyanta da igiya ta hanyar rataya.

href="https://www.hindustantimes.com/india-news/28yrold-killed-by-husband-in-up-for-refusing-to-convert-say-police-101635615002059.html">Jaridar Hindustan Times ta ce Mahaifiyar matar Kaushal Devi ce ta shigar da ƙara ofishin ƴan sanda tana mai zargin surukinta da kashe ƴarta.

Ta ce sun yi aure shekaru 10 da suka gabata, kuma mijin ya yi iƙirarin cewa shi Hindu ne, daga baya ne matarsa ta gano asalin addininsa. Sun haifi ƴaƴa biyu mata, amma ya ci gaba da tursasawa matarsa dole sai ta musulunta, kamar yadda mahaifiyar matar ta bayyana.

Ƴan sanda sun ce sun shigar da ƙara kotu game da batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *