Lars Vilks, Mutumin da yayi zanen ɓatanci ga Annabiﷺ ya mutu sakamakon haɗarin jirgin sama a ƙasar Sweden.

Rahotanni sun tabbatarda mutuwar Lars Vilks, mutumin da ya zana hoton Annabi Muhammadu (SAW) da zummar ɓatanci a shekarar 2007.

Lars Vilks mai shekaru 75 ɗan Asalin ƙasar Sweden ya mutu ne a yammacin jiya Lahadi sakamakon haɗarin jirgin sama da ya rutsa da shi.

Rahotanni daga ƙasar ta Sweden sun bayyana cewa haryanzu ana cigaba da binciken musabbabin faruwar haɗarin.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *