Taliban sun haramtawa gidajen TV a Afghanistan amfani da mata ƴan jaridu a matsayin masu gabatar da shirye-shirye ko labarai.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Ƙngiyar Taliban sun sake sanar da sabuwar doka tare da shata layi ga shafukan watsa Labarai na Akwatin Talabijin (TV) inda suka gargaɗesu da su daina barin mata suna gabatar da shirye-shirye.

Ma’aikatar gyaran ɗabi’u da daukaka darajar al’amuran wadda take ƙarƙashin kulawar Taliban ta wallafa wannan sanarwa cikin wani shirin Radiyo daya gabata jiya Lahadi.

Taliban sun gargaɗi cewa ya zama wajibi kowanne gidan Talabijin ya kaucewa yin amfani da mata yayin gabatar da shirye-shirye.

A

baya ma ƙungiyar ta Taliban dake ƙasar Afghanistan ta bayyana cewa duk matan da suke karatu a Jami’o’i ya zama wajibi su rinƙa yin shiga dai-dai da koyarwar addinin Islama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *