‘Yar majalisar dokokin Amurka musulma Ilhan Omar, ta gabatar da kudirin doka tana neman a hana sayar da makamai masu linzami na sama da dala miliyan 650 ga kasar Saudi Arabiya.

‘Yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Omar, ta shigar da wata doka a ranar Juma’a, tana neman hana sayar da makamai masu linzami na sama da dala miliyan 650 ga Saudi Arabiya, wanda shi ne na farko da aka sayar wa masarautar a lokacin gwamnatin shugaba Joe Biden.

Omar ta ce ta gabatar da wannan matakin, wanda aka fi sani da kudurin kin amincewa da hadin gwiwa, saboda rawar da Saudiyya ke takawa a yakin basasar Yemen, wanda ake daukarsa a matsayin daya daga cikin bala’o’in jin kai a yakin duniya, da kuma yadda ake take hakkin bil’adama.

Gwamnatin

Biden ta sanar a ranar 4 ga Nuwamba cewa ta amince da siyar da makami mai linzami na iska zuwa iska 280 wanda darajarsu ta kai dala miliyan 650. Raytheon Technologies (RTX.N) ya kera makamai masu linzami.

“Bai kamata mu taba sayar da makamai ga masu take hakkin bil’adama ba, amma tabbas bai kamata mu kasance muna yin hakan ba ga wdanda suke taka rawa a tada rikici ga bil’adama. Majalisa na da ikon dakatar da wannan cinikin, kuma dole ne mu yi amfani da wannan ikon,” in ji Omar. a cikin wata sanarwa.

Hasashen matakin na dakatar da siyarwar ya yi kadan, tunda ya zama dole ya wuce majalisar dattawan Amurka kuma ya tsira daga matakin veto. Amma matakin na Omar ya jaddada ci gaba da taka-tsan-tsan game da sayar da makamai ga Riyadh a tsakanin wasu ‘yan majalisar dokoki, duk da aniyar gwamnatin Biden na takaita siyar da makamai ga masarautar zuwa kayayyakin kariya.

Yayin da Saudiyya ke zama muhimmiyar abokiyar kawance a Gabas ta Tsakiya, ‘yan majalisar dokokin Amurka sun ki amincewa da yawan sayar da makamai ga masarautar ba tare da tabbacin ba za a yi amfani da kayan Amurka wajen kashe fararen hula ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *