Yaron tsohon Shugaban ƙasar Libya, Gaddafi ya shiga cikin jerin masu neman takarar Shugabancin ƙasar a zaɓen da za’a gudanar watan Disamba.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Seif al-Islam Gaddafi, yaron tsohon Shugaban ƙasar Libya Moamer Gaddafi ya shiga jerin ƴan takarar Shugabancin ƙasar a zaɓen da ake shirin gudanarwa a watan Disamba.

Seif al-Islam Gaddafi ya karɓi shaidar tsayawa takarar ne daga ofishin gudanarda harkokin zaɓe dake birnin Sebha a kuduncin ƙasar ta Libya.

An kuma tabbatarda cewa ya samu dukkan shaidu tare da cika sharuɗan tsayawa takarar kamar dai kowanne ɗan takara.

A karon farko ne ake tsammanin ƙasar Libya zata fara gudanar da zaɓe domin fidda sabon Shugaban ƙasar bayan rikice-rikicen da ƙasar tayi fama dashi tun bayan da aka kashe tsohon Shugaban ƙasar wato Muamer Gaddafi a shekarar 2011.

Har’ilyau;

cikin wata tattauna da ɗan takarar mai suna al-Islam yayi da manema labaru, ya bayyana cewa babban burinsa idan ya samu nasarar cin zaɓe shine ɗabbaka zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma wanda a baya aka fuskanci ƙarancinsa tsawon loƙaci a faɗin kasar ta Libya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *