A cikin kowace awa daya (1hr) sai da Nigeria tayi asarar Zunzurutun Kudi Naira Miliyan Dari da Hudu da digo biyu, (104.2) sakamakon dakatar da twitter.


Idan ba’a manta ba, a ranar 4 ga watan June, 2021 gwamnatin Nigeria ta dakatar da kafatanin ayyukan kamfanin Twitter a Nigeria sakamakon wani Sako da Kamfanin ya gogewa Shugaban kasar Nigeria wanda suna ganin wallafa sakon ya saba da dokokin su, inda hakan ya fusata shugaban Kasar har ta kaiga ya bada umarnin dakatar da ayyukan Kamfanin.

Daman Wannan ba sabon Abu bane a wurin Kamfanin na Twitter domin kuwa irin haka ta taba faruwa da tsohon Shugaban Kasar America Donald Trump inda Kamfanin na Twitter shima ya goge masa wani sako da ya wallafa a lokacin yana Shugaban Kasar ta America.

Bayan

dakatar da ayyukan na Twitter Masana da dama sun ankarar da Shugaban Kasa akan irin asarar da Nigeria zata tafka sakamakon dakatarwar, saidai Shugaban Kasar bai kalli Wannan Shawarar ba, hakan tasa Kamfanin na twitter saida ya share kimanin watanni 7 baya aiki a Nigeria.

Kamar yadda NetBlocks Cost of Shutdown Tool suka bada kididdiga shine: Kasar mu ta Nigeria tana asarar zunzurutun Kudi da suka kai Naira Miliyan Dari da Hudu da digo biyu (N104.2 Million) a duk awa daya (1hour) da Kamfanin yayi a rufe, hakan yana nuna cewa duk kwana daya da Twitter tayi bata aiki a Nigeria muna asarar kudi kimanin Biliyan biyu da digo arba’in da Shida (N2.46 billion).

Idan muka lissafa zamuga Kamfanin na Twitter ya share awanni dubu biyar da Dari Uku da Ashirin da takwas (5,328 hours) baya aiki a Nigeria, wadannan awanni sune zasu baka kwanaki Dari biyu da Ashirin da Biyu (222) to idan muka hada lissafin Jimilla zamuga cewa Nigeria tayi asarar kudi kimanin Naira Biliyan Dari Biyar da Arba’in da Shida da digo Biyar (N546.5 billion) wanda hakan ba karamin ci baya bane ga tattalin arzikin Kasa.

Inda Shikuma Kamfanin Na Twitter ban samu kididdigar asarar da yayi ba, saidai bansan ko zamu iya samu ba a wurin Abdulrazak Rogo ko Mohiddeen Ahmad.

Shehu Rahinat Na’Allah
13th January, 2022.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *