Idan za ayi magana ta gaskiya babu Gwamnatin data Dada rusa harkar kasuwanci a Jihar Kano kamar Gwamnatin Ganduje – Alhaji Liti Kul-kul.

Tsohon Shugaban yan’ kasuwar Kantin Kwari dake Jihar Kano Alhaji Liti Kulkul ya ce idan za ayi magana ta gaskiya babu Gwamnatin da ta dada rusa harkar kasuwanci a Jihar Kano kamar Gwamnatin Ganduje.

Ya yi bayani ne biyo bayan tsokaci akan yajin aikin da yan” kungiyar adaidaita Sahu sukeyi saboda matsin lamba da suka CE Gwamnatin ta Ganduje nayi musu.

Liti Kulkul yace tun ranar da yan’ adaidaita Sahun suka tafi yajin aikin idan ka duba duk kasuwannin Jihar sunyi fayau, duk wasu baki da suke shigowa Jihar siyayya sunki zuwa saboda tunanin abin hawan dazasu Dora kayan da in suka siya zasu kaisu har tasha.

Daga

Kabiru Ado Muhd
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *