Mun Kusa Mu Hana Shigo Da Madara Da Kifi Najeriya, Inji Gwamnatin Tarayya.

Da sannu zamu dakatar da shigo da kifi, madara, FG.

Gwamnatin tarayya a ranar Talata, ta ce nan ba da dadewa ba za ta hana shigo da kifi da madara cikin kasarnan.

Ministan Noma da Albarkatun Kasa, Sabo Nanono ne ya bayyana hakan a wajen kaddamarwar da aka shirya na cibiyar shirya kayan masarufi (AIC) a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, a Jihar Jigawa.

Nanono ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kara duba duk wani shigo da abinci cikin kasar.

Ministan ya bayyana cewa an albarkaci Najeriya da dimbin albarkatu da dama, yana mai jaddada cewa babu wani abu da ake shigowa da shi wanda ba a samar da shi a kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *