Ruwan leda (Pure Water) ya koma N20.

Kungiyar masu samar da ruwan leda (pure water) reshen jihar Kogi ta sanar da karin farashin ruwan leda da aka fi sani da “Pure Water” daga Naira 10 zuwa N20.

Masu samar da ruwan sun danganta matakin nasu da tsadar kayan da ake samu sakamakon canjin Naira zuwa Dala.

Kungiyar ta kara adadin kudin ledar ‘pure water’ a shekarar da ta gabata daga N100 zuwa N130 sakamakon abin da ATWAP ke kira da tasirin tattalin arzikin da annobar COVID-19 ta fara yi.

Shugaban

kungiyar, Mista Joseph Eseyin ya sanar da haka a wata tattaunawa da Jaridar Dailytrust a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Ya ce yanzu za a siyar da ledar ruwan akan Naira 200 saboda halin da ake ciki na tattalin arziki.

Ya kara da cewa, matakin ba wai yana nufin kawo wa masu amfani da wahala ba ne, illa dai don rage illar tsadar kayayyaki da ake samu da kuma baiwa ‘yan kungiyar damar samar da ruwan sha wanda ya dace da tsarin hukumar kula da magunguna ta kasa.

Eseyin ya kara da cewa litar man fetur ya karu zuwa N165.

Ya kara da cewa da sabon farashin ruwan pure water zai zama N20 a fadin jihar ta Kogi. Eseyin ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da su ba kungiyar hadin kai a sabon tsarin farashin.

Eseyin ya jaddada cewa ATWAP na shirin gudanar da atisayen tsaftar muhalli na kwanaki 3 domin ba su damar samar da isassun tsari a kasa domin yiwa masu amfani da shi hidima a jihar.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *