Wasu ‘yan kasuwa a Kano sun daina siyar da kayansu saboda tsadar Dalar Amurka.

Ratonni daga kasuwar kantin kwari dake jihar Kano na cewa wasu ‘yan kasuwa sun dakatar da siyar da kayansu saboda rashin tsayayyen farashin Dalar Amurka.

‘Yan kasuwar sun ce baya ga rashin tsayayyen farashi, haka kuma Dalar tana matukar wahalar samu a kasuwar musayar kudaden waje.

Wani dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Jaridar Mikiya cewa a halin yanzu ba zai yiwu su cigaba da siyar da kaya ba, saboda wasunsu kayan ba na su bane, na mutanen China ne suka karbo bashi, kuma lissafin bashin nasu ba da Naira bane, da Dala ne.

Dan

kasuwar ya kara da cewa su kuma wadanda suke da jarinsu na kansu idan suka siyar da kayansu dole sai sun cika makudan kudade kafin su siyo wasu, wanda hakan na iya durkusar da harkokin Kasuwancinsu ta hanyar karancin kayan da za su siyo da kudin.

Dan kasuwar ya ce sun dauki matakin dakatar da siyar da kayan ne daga nan zuwa lokacin da farashin Dalar zai daidaita.

A jiya Alhamis dai an siyar da Dalar Amurka a kasuwar musayar kudaden waje ta jihar Kano dake Fagge a kan Naira 572.

A kwanakin nan dai Dalar Amurka tana ta hauhawa, wanda hakan yajawo tashin kayayyakin amfanin yau da kullum a Najeriya.

‘Yan kasuwar sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa akan wannan al’amarin na tsadar ta hanyar samar musu da dala mai sauki daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *