TIRƘASHI: An bayyana yaro ɗan Shekara 13 da yayi wa Facebook, WhatsApp da Instagram kutse salon zarga-gum-gum.

A ranar 4 ga Oktoba 2021, Facebook, Messenger, WhatsApp da Instagram duk suka tsaya cak game da amsa da aika saƙo ta kafofin sada zumunta sauka na kusan awanni shida.

Wasu shafukan yanar gizo da shafukan Facebook sun fara iƙirarin cewa rashin nasarar ya faru ne saboda wani ɗan fashin kwamfuta dan China ɗan shekara 13 mai suna “Sun Jisu“.

Kafofin watsa labarai na duniya sun yi iƙirarin cewa “China” ce ke bayan dakatar da ayyukan kafofin sadarwar ta zamani a faɗin duniya a wannan rana.

A

cewar kamfanin dillacin labarai na Reuters, wani dan Dandatsa ɗan kasar China mai suna “Sun Jisu” shine ke da alhakin dakatar da ayyukan “Facebook“, “WhatsApp” da Instagram, sannan ya ƙara da cewa mai satar bayanan na China, shekarun sa 13 ne kacal.

Shi wannan mai fashin na kwamfutar na ƙasar Sin “Sun Ji Su” yanzu ya zama babu tamkar sa a kan shahararrun injunan bincike irin su goggle da kafar sadarwa ta Twitter a cikin mintuna da suka gabata, bayan da ya katse WhatsApp, Instagram da Facebook a duk ƙasashen duniya, duk saboda tambayoyin da mutane ke yi game da cikakkun bayanan wannan labarin.

Ɗan Dandatsar na ƙasar Sin wanda ya hargitsa Facebook, WhatsApp da Instagram a duniya.

Sun Jisu, wanda ya yi kutse a shafukan guda uku shine dai ya sa aka hana ma’aikatan Facebook shiga hedikwatar cibiyar ta duniya bayan da aka toshe tashoshin lantarki kuma ya haifar da asarar tattalin arziki da aka kiyasta biliyoyin daloli a duniya.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *