Duk wata kafar sadarwa ta zamani, dole ne tayi rijista da gwamnati.

Lai Muhammad

Idan za’a iya tunawa a ƴan kwanakin nan, gwamnatin tarayya ta samu sabani tsakaninta da kamfanin sadarwar nan na zamani mai suna Tuwita.

Inda takai ta kawo, Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe amfani da kamfanin a kafatanin ƙasar mai ɗauke da masu bibiyar shafin sama da miliyan arba’in.

To sai dai da alama, hakan yasa gwamnatin tunanin canja fasalin yadda ake gudanar al’amuran kafafen sadarwar domin gujewa sake faruwar hakan anan gaba.

Hakan shine dalilin da gwamnatin tarayya ta bada sanarwa akan cewa, dole ne duk wani kamfani na sadarwa da suka haɗa da Facebook, twitter da sauransu akan suyi rijista da gwamnati domin ci gaba da gudanar da harƙallar su a ƙasar.

Batun ya fito ne daga bakin ministan sadarwa na ƙasa, Lai Muhammad.

Hakan na nufin kenan, duk kamfanin daya bijire wa yin wannan rijista, ko kuma yaƙi yi kwata kwata zai iya fuskantar fushin gwamnatin ta hanyar rufe kamfanin , wanda hakan zai iya haddasa musu gagarumar asara duba da yadda Najeriya take a matsayin babbar ƙasa da ake ji da ita a harkar gudanarwa ta sadarwa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *