Hukumar ƴan Sanda ta ƙasa ta buɗe shafi domin yin rijista ga matasa masu sha’awar shiga aikin ɗan Sanda.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Hukumar ƴan Sanda ta ƙasa NPF ta bayyana buɗe shafi domin masu sha’awar aikin Ɗan sanda su yi rijista.

A cewar rahotannin, an tabbatarda cewa za’a ɗauki adadin sati 6 kafin a rufe shafin.

Ga masu sha’awar yin rijista zasu iya bibiyar shafin ta wannan adireshin www.policerecruitment.gov.ng

Abubuwan da ake buƙata ga mai sha’awar yin rijista sun haɗa da;

1- Lambar katin shaidar dan kasa (NIN)
2- Ga mai sha’awar rijista, dole ya tabbata yana da cikakken makin “C” a Turanci da Lissafi cikin Jarrabawar WAEC ko NECO.
3- Dole ya zama tsakanin Shekaru 17-25
4-

Dole mutum ya kasance mai cikakkiyar lafiya a zahirance da hankalce.
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *