Matsalar Rashin Tsaro A Najeriya: Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Ɗage Gagarumin Taron Ƙarawa Juna Sani “National Seminar” Da Ta Shirya Gudanarwa Na Tsawon Kwanaki Biyu A Jihar Gombe

Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban Ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, ta ɗage gagarumin taron ƙarawa juna sani “National Seminar” wanda ba’a taɓa gudanar da irin shi ba a Najeriya, da ta shirya gudanarwa na tsawon kwanaki Biyu a jihar Gombe.

Idan baku manta ba Ƙungiyar ta shirya gudanar da taron ne a ranar 4 ga watan yuni 04/06/2021, a rufe a ranar 6 ga watan Yuni 06/06/2021.

Ƙungiyar

ta shirya gudanar da taron ne don horar da Marubutan jihohin Arewa game da yadda ake rubutu da kuma amfani da kafofin Sadarwar zamani, don ganin an tsaftace harkar rubuce-rubuce a kafofin sadarwar zamani.

Taken Taron: “Rawar Da Kafofin Sada Zumunta Ke Takawa, Da Cigaban Yankin Arewa Musamman Rashin Tsaro, Durƙushewar Tattalin Arziƙin Ƙasa, Siyasa Da Haɗin Kan Al’umma.”

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta ɗage taron ne duba da yadda rashin tsaro yayi muni a wasu manyan jihohin Arewa cikin ƴan kwanakin nan dama ƙasar baki ɗaya.

Ƙungiyar ta tattauna da hukumomin tsaro tare da karbar shawarwarin masana tsaron, duba da yanayin hanyoyin da mahalarta taron da dama zasu biyo a wannan yanayin da ake ciki na ƙara taɓarɓarewar rashin tsaro a yankin Arewa dama ƙasar baki ɗaya.

Da wannan babban dalilin ne Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta ɗage gagarumin taron da ta shirya gudanarwa har zuwa lokacin da za’a samu zaman lafiya.

“Arewa Media Writers” tana Addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa a yankinmu na Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.

Haka zalika Ƙungiyar tana buƙatan Addu’o’inku kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba na ganin ta tsabtace harkar rubuce rubuce a kafofin sadarwar zamani. Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *