Mayaƙan ISWAP sun kashe Kwamandoji 2 tare da ƙarin ƴan ta’adda 15 a wani mummunan hari da suka kai sansanin Boko Haram.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe Kwamandojin Boko Haram 2 waɗanda suka haɗa da Amir Modou Marte, Amir Moustapha Baga tare da wasu 15 daga cikin mayaƙan na Boko Haram.

Kamar yadda rahoto yazo a PRNigeria, wannan artabu ya faru ne jiya Lititin a Toumboun Gadura’a dake kusa da tafkin Chadi a Jihar Borno.

Jaridar Mikiya ta gano cewa ƙungiyoyin biyu, Boko Haram da ISWAP sun ɗauki dogon loƙaci suna kashe junansu, sakamakon rikicin Shugabanci wanda ya ɓarke kuma shine silar mutuwar Shuwagabanninsu guda biyu, wato Abubakar Shekau da Abu Musab Albarnawi.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *