Ya faɗo daga bene mai hawa tara amma da mutane suka kewaye shi suna taraddadin abin da ya faru ya miƙe zumbur tare da tambayar su wai mai yake faruwa ne.

Wani mutum ya tsira daga faɗuwar da yayi daga wani katafaren gini a New Jersey, Amurka da safiyar Laraba, 6 ga watan Oktoba, inda har yanzu lamarin da yake ci gaba da ba mutane mamaki.

Mutumin mai shekaru 31 ya faɗo ne daga wani bene mai hawa tara kafin daga bisani ya faɗo kan saman wata mota da aka ajiye a ƙasan ginin ƙirar BMW, kamar yadda rahoton New York Post ya bayyana.

class="has-text-align-justify">To sai dai bayan faɗuwar da yayi ne a saman motar, motar tayi masa katifa salon dunlop, inda da saukarsa kuma ta taimaka masa ya tsira, ba tare da ya karye ba ko kuma yaji mugayen raunuka.

Abin mamaki, lokacin da masu kallo suka matso bayan faɗuwar tasa, sun lura yana nan da rai, bai mutu ba.

Daga nan ya miƙe a cikin ɓaragusan motocin, ya ɗaga hannunsa na dama, ya soma tambayar waɗanda ke tsaye, “Me ya faru ne?”

Wata baiwar Allah mai shaidar gani da ido, Christina Smith, ta kira 911 don taimako. Inda aka gano cewa mutumin ba aiki bane yakaisa ginin ba, sannan kuma tun daga lokacin da abinda ya faru ya ƙi bai wa ƴan sanda sunansa.

Na ji babban tashin hankali kuma ban yi tsammanin mutum ne da farko ba. Tagar baya ta motar kawai ta tayi kwatsa kwatsa. Kutsum, sai mutumin ya yi tsalle ya fara ihu. Hannunsa duk sun jigata, ” in ji Smith.

Daga baya ne da akayi bincike, duk da haka, yana cikin mawuyacin hali a wani asibiti da ke kusa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *