ƙaddara ko Ganganci: Wani inyamuri ya ɗirkawa wata bahaushiya cikin shege a jihar Kebbi.

Jami’an tsaro sun gabatar da wani inyamuri mai suna Onyebuchi Okafor a gaban kotun majistiri mai lamba ɗaya wacce Sama’ila Kakale Mungadi ke jagoranta.

Kamar yadda jami’an ƴan sanda suka gabatar,
Onyebuchi Okafor ana zargi gamida tuhumarsa ne da ɗirkawa wata yarinya mai suna Mansura Shehu cikin shege, wanda idan aka duba kundin Penal code sashi na 369, ya haramta hakan.

class="has-text-align-justify">Tun kafin nan ranar 17 ga watan Yuni ne jami’an rundunar musulunci ta Hisba ta fara gayyatar Onyebuchi abisa wannan zargin.

Koda gama binciken na Hisba ne sai suka miƙa binciken nasu ga rundunar ƴan sanda ta jihar Kebbi domin cigaba da gudanar da bincike

Bayan da ƴan sanda suka shigar da ƙarar ne a kotu kamar yadda doka ta samar, sai mai Shari’a Sama’ila Kakale Mungadi, ya bawa jami’an tsaro damar su cigaba da tsare Onyebuchi da Mansura a bayan kanta har zuwa 5 ga watan Yuli Mai kamawa domin cigaba da gudanar da shari’ar.

To sai dai mai kare Onyebuchi a shari’ar, ya nemi mai Shari’a Sama’ila Kakale Mungadi daya taimaka ya bawa wanda ake zargi beli amma tuni alkalin yayi fatali da wannan buƙata, saboda haka akayi gaba dasu zuwa wannan rana.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *