ƴan fashi da masu garkuwa da mutane su ne manyan kwastomomin mu, ina samun ₦70,000 a kullum inji mai kaiwa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai burodi.

Daya daga cikin masu gasa biredin lokacin da yake ba da burodi ga ƴan fashi ya bayyana ƴan fashi da makami da ke tsoratar da mazauna Kaduna da kewaye a matsayin mafi kyawun abokan cinikin su.

Wasu masu gasa burodi uku, wadanda ƴan sanda suka cafke a Kaduna, sun yi iƙirarin cewa suna baiwa yan fashi burodi a farashin mai nauyi inda su kuma suke cin gwagwgwaɓar riba.

Magaji na ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, ya faɗawa jami’an tsaro cewar:


“Na fuskanci duk sanda sukayi kamu mai yawa bukatar buredi na ƙaruwa sosai, kamar lokacin da suka kama wasu ƴan jami’a ne, nakan siyar musu da biredi na dubu saba’in kullum, amma yanzu abin yayi ƙasa. baifi na dubu hamsin nake siyar musu ba a kullum, inji Magagi.”.

Kamar yadda bincike ya nuna ƴan fashin suna gudanar da ayyukansu ne a sansanonin Damari, Kidandan da Awala da ke cikin garin Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Waɗanda ake zargin sun jagoranci ƴan sanda zuwa gidan burodi inda aka kame burodin gamida garƙame gidan.

Masu garkuwa da jama’a da fashi da makami sun addabi ilahirin garuruwan dake arewacin Nijeriya, wanda haka ya gurgurtan da harkokin tsaro da kuma na tattalin arziki.


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

One thought on “ƴan fashi da masu garkuwa da mutane su ne manyan kwastomomin mu, ina samun ₦70,000 a kullum inji mai kaiwa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai burodi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *