1. Yadda zaka iya kudancewa da wurwuri, 2. yadda ake wajoko — Na daya daga cikin bincike guda 15 da ƴan Najeriya sufi nema a yanar gizo

Haikika fitowar yanar gizo gizo ya sauya wasu abubuwa na har abada. Salon yadda muke sadar da zumunci, kasuwanci, ilimi, nishadi da sauran abubuwan fannin rayuwa na yau da kullum.

Hakan ne yasa mutane ke zurfafa bincike domin samun ilimi akan abinda basu sani, koda kuwa abin ya kasance ya kirki ne da akasin haka. Tunda yanzu, wayoyi sun kasance gidan kowa da akwai, kuma fasahar yanar gizo gizo ta zama gidan kowa da akwai.

class="has-text-align-justify">Hakan ne yakai ga yin wani binciken kwakwaf na yadda yan najeriya ke , ta’ammali da yanar-gizo-gizo cikin shekaru 15 da suka wuce.

Wannan sakamakon binciken na kwakwaf da aka gudanar ya lissafo abubuwan da ƴan Najeriya suka fi nema a yayin da suke ninkaya a yanar gizo cikin shekaru 15 da suka wuce.

Bisa ga sakamakon binciken:

  1. Menene Soyayya
  2. Yadda ake jima’i
  3. Menene na’ura mai kwakwalwa
  4. Yadda ake rubuta wasikar neman aiki
  5. Menene karatun halitta,
  6. Yaya tsadan dala da Naira
  7. Yadda za ka iya kuɗancewa na-da-nan a yanar gizo

Sai kuma waɗanda suke bi musu sun haɗa da

8. binciken labarai

9. harkokin siyasa daga ingantattun gidajen jaridu.

A fannin nishadi kuma ƴan Najeriya na yawan neman kalmomin wakoki kamar su;

Xxxtentacion Bad Vibes Forever, In Christ Alone lyrics, Brown Skin Girl, All Of Me, Onise Iyanu, Reckless Love, Despacito, Silent Night, Great Is Thy Faithfulness da Ancient Words.

Shahararrun ƴan fina-finan Nollywood da Kannywood da ƴan Najeriya suka nema a ƴanar gizo cikin waɗannan shekaru sun haɗa da:

Mercy Johnson, Funke Akindele, Ini Edo, Odunlade Adekola, Adam A Zango, Iyabo Ojo, Rita Dominic, Angela Okorie, Juliet Ibrahim da Adunni Ade.

Mawakan Najeriya da aka fi nema a yanar gizo sun haɗa da

Burna Boy, Omah Lay, Adekunle Gold, Tope Alabi, Small Doctor, Reekado Banks, Banky W, Frank Edward, 2Face Idibia da Yinka Ayefele.

Mawakan kasashen waje da ƴan Najeriya suka fi nema a yanar gizo

Nicki Minaj, Chris Brown, Cardi B, Ariana Grande, Kanye West, Celine Dion, Meek Mill, Bob Marley, Whitney Houston da August Alsina

Yadda ake haɗa abinci da kayan kwalama

Pornstar martini cocktail recipe, Cake recipe, Pancake recipe, Meat pie recipe, Puff puff recipe, Chocolate cake recipe, Doughnut recipe, Chin chin recipe, Fried rice recipe da Red velvet cake recipe.

Fina-finai na ciki da kasashen waje da aka fi neman su a yanar gizo

Sex and the city movie, The BFG movie, Titanic movie, Black panther full movie, Moana, Frozen 2, Kesari Yoruba movie, Half of a Yellow Sun movie, War room movie da Fifty Shades of Grey movie.

Dabarun hana kiba a jiki

Ketogenic diet, Cambridge diet, Hallelujah diet, Dash diet, Atkins diet, Paleo diet, Diabetic diet, Mediterranean diet, Vegan diet da Ulcer diet

Sannan kuma a Kwallon kafa, an fi neman kungiyoyin kwallon kafa kamar su:

Man U, Real Madrid, Chelsea FC, Arsenal FC, Man City, FC Barcelona, Liverpool FC da AC Milan

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *