2022 dole Gwamnatin Tarayya ta fito da Sabuwar Hanyar taimakon kirkire-kirkiren fasahar zamanin matasa ~Cewar Sanata Uba sani

A wani sako daya fitar na Sabuwar Shekarar 2022 Sanata Malam Uba Sani na kaduna ta tsakiya Yana Cewa Ina yi wa ’yan uwana maza da mata barka da zuwa Sabuwar Shekarar 2022. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya nuna mana wannan sabuwar shekara da fatan zamu Sanya wannan Shekara ta 2022 ta zama shekara domin tunawarmu. mu yi amfani da wannan lokacin domin inganta rayuwarmu da ciyar da kasarmu gaba.

2021

shekara ce data kunshi abubuwan tunawa marasa daɗi. Tilas tsarinmu a 2022 ya bambanta. Kada mu kasance fursunoni na abubuwan da basu da daɗi a baya. Dole ne mu yi ƙoƙarin kawar da kanmu daga munanan abubuwan da muke fuskanta kuma mu ci gaba da sabon salo. Akwai damarmaki a Gaba suna jiran mu muyi nazari mu bincika. Amma duk ya dogara da zaɓin da muka yi a yanzu.

Mu kuduri aniyar haduwa a cikin al’ummarmu domin samun maslaha. Rashin ha’din kai ba zai iya ciyar da al’ummarmu gaba ba. Hanyar shawara ga juna ita ce hanya mafi kyau. Dole ne mu samar da ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin ba mu damar samun shiga tsakani na Gwamnatin Tarayya na kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs), musamman a fannin Noma. Inji Sanatan.

Sanata Uba Sani Ya Kara da Cewa Dole ne gwamnatoci a matakin tarayya da na jihohi su samar da hanyoyin da za su taimaka wa al’ummarmu, musamman ma matasa su gane abubuwan da suke da shi na baiwa. Dole ne mu daina murkushe fasahar kirkire-kirkire musamman kirkire-kirkiren fasahar zamani ta Kai da Kai na matasan mu. Najeriya tana alfahari da wasu matasa masu hazakar kirkire-kirkire da sabbin dabaru a duniya. Musamman a fannin Fasahar Sadarwar Zamani ICT) da Start – Ups Lamarin na ban mamaki. Abin da ya rasa duk da haka shine goyon baya mai dorewa daga gwamnati da ƙungiyoyin kamfanoni. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da 2022 “Shekara don Karfafa Tattalin Arzikin Matasa.” Yakamata Gwamnatin Tarayya ta samar da cikakkun bayanai da goyon baya na “Youth Start – Ups,” musamman a bangaren ICT da kuma fito da wani babban shiri na shiga tsakani domin magance kalubalen kudi. Idan mukayi kokari Mai nagarta tabbas Najeriya za ta iya gogawa ta kalubalanci matakin mamayar Amurka da Indiya a fannin ICT.

Har’ila Yau Kuma Shekarar 2022 ta sake baiwa ‘yan siyasar Najeriya wata dama ta sake jan hankalin al’ummar Najeriya da kuma dawo da kwarin gwiwa da amanarsu. Jama’ar Najeriya sun ba da amanarsu a gare mu amma mun kasa mayar da martani a garesu Ayyukanmu da rashin ayyukanmu sun lalata dimokuradiyyar mu kuma sun sa mutane da yawa sun rabu da tsarin siyasa. Dole ne mu kuduri aniyar yin gyara ga jama’a. Dole ne mu sake rungumar siyasar da’a da dabi’u. Kada mu ci gaba da neman nasara saboda mulki. Dole ne mu nemi mulki domin inganta yanayin jama’a da kuma samar da kasarmu ta zama mafi kyawun rayuwa. Mu ci gaba da bunkasa sa ta domin ci gaban al’ummarmu da kasarmu.

Dole ne jami’an tsaron mu su yi taka-tsan-tsan kan dabarun da suka bi wajen yakar ta’addanci, tada kayar baya, ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in laifuka a 2021. Akwai bukatar sabbin tunani da sabbin abubuwa cikin gaggawa. Dole ne kuma su sake jajircewa wajen yakar su kuma su kuduri aniyar murkushe masu aikata laifuka gabaki daya. Dole ne a yi sabin matakan a 2022. Bugu da ƙari, dole ne Gwamnatin Tarayya ta himmatu ga dukan ‘yan Najeriya don tallafawa yaki da ta’addanci. Da zarar an hana ‘yan ta’addan goyon baya na cikin gida, za a cinye wa’adin kwanakinsu.

Ina yiwa ‘yan mazabana, nagari mutanen shiyyar Sanatan Kaduna ta tsakiya fatan alheri a 2022. Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen ganin na canza salon siyasar mazabar. Rashin tsaro ya dakushe ci gabanmu. Na dade ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gudanar da ayyuka na musamman a kananan hukumomin mu da abin ya shafa. Na yi imani da cewa hukumomi za su yi iya kokari a 2022 domin ganin rayuwa ta dawo daidai a cikin al’ummominmu kada mu yanke kauna. Mu yi ƙoƙarce-ƙoƙarce don yin abin da ya dace daga halin da ake ciki. Mu mutane ne masu juriya. Za mu shawo kan kalubalen mu, mu mai da musibarmu da Matsalar mu zuwa ci gaba Mai dorewa. Inji Sanata Uba Sani

Barka da sabuwar shekara!!!

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *